Matar Tsohon Shugaban Kasa Jonathan, Ta Halacci Bikin Taron Kaddamar Da Littafi Kan Yaki Da Cin Hanci


Taro ya rude da tafi da kuma sowa lokacin da aka hangi Patience Jonathan, matar tsohon Shugaban kasa Gudluck Jonathan a wurin taron kaddamar da littafi kan cin hanci da rashawa mai suna “Antidotes for corruption, the Nigerian story ‘ a turance wanda Sanata Dino Melaye ya rubuta.

Uwargida Patience na fuskantar zarge zarge daga hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’anati ta EFCC, kan halarta kudin haram wanda har ya jawo hukumar ta nemi kotu da ta rufe wasu asusun ajiyar banki guda biyu dake dauke da miliyoyin dalolin Amurika.

Patience ta samu tarba daga kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da kuma shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki. 

You may also like