Matasa 6 Sun Rasa Ransu A Wajen Haƙar Lakar Gini A Jihar Sokoto


An samu mutuwar mutum shida a lokacin da suke ginar laka a wani guri da aka kebe don dibar lakar gini a garin Kalmalo dake karamar hukumar Illela a jihar Sokoto.

Mamatan su shida sune kamar haka;

1. Bashar Alh. Dalhatu
2.Bashar Maciji,
3.Bashar Alh. Buhari,
4.Isah Alh. Amadu
5.Abdullahi Salihu,
6.Bilyaminu Alh. Jadi

Dukkansu matasa ne ‘yan kasa da shekara Talatin da haihuwa, sun samu kansu ne a cikin wannan ramin don taya daya daga cikin abokinsu da ke shirin aure a ‘yan kwanaki masu zuwa.

An gudanar da jana’izar su bayan sallar Juma’a, inda Shugaban Karamar Hukumar Mulkin Illela Alh. Abdullahi Haruna Illela, Hon. Alhaji Dayyabu Adamu Kalmalo, Wakilin Sarkin Rafin Illela (Alh. Sahabi Isah Illela), Alh. Abubakar Abdullahi (Ubandawakin Illela) Galadiman Illela (Alh. Aminu A Musa Illela), S. A. (Alh. Ibrahim Ismailah Kalmalo), Walin Illela (Alh. Sanusi Wali), Kansilolin Mazabar Kalmalo da Illela (Mal. Hon. Hamza Kalmalo da Hon. Kabiru Mohammad Illela suka halarci jana’izarsu.

Allah ya jikansu, ameen

You may also like