kungiyoyin matasa da dama ne suka halacci taron gangamin da akayi yau a fadar Sarkin Daura dake garin na Daura mahaifar shugaba muhammadu Buhari don nuna goyon bayansu ga shugaban da kuma murnarsu bisa dawowarsa gida lafiya.
Taron ya samu halaccin Sanata mai wakiltar Katsina ta Arewa Mustafa Bukar, inda yayi kira da yan Najeriya dasu kara hakuri domin gwamnatin Buhari na aiki tukuru don ganin ta dora kasarnan kan hanyar cigaba mai dorewa, shima anasa jawabin kwamishinan sharia na jihar Alhaji Ahmed Marzuk wanda ya wakilci gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana shugaba Buhari a matsayin shugaba wanda yazo da shiri na musamman don cigaban Najeriya inda yace duk wadanda sukewa shugaban fatan mutuwa to makiyan Najeriya.
Yau dai kwanaki 8 da daowar shugaban daga birnin London na kasar Burtaniya inda likitoci suka duba lafiyarsa.