Matasa da suka fusata sun rufe hanyar Kaduna zuwa Abuja


Hakkin mallakar hoto:Sumner Shagari Sambo

Matasan kauyen Sabon Gaya dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sun fusata   inda suka rufe hanyar bayan wasu yan bindiga suka kashe wani mutum dan kungiyar samar da tsaro ta sa kai dake garin.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa matashin da aka kashe wanda aka ki bayyana sunansa ya tafi gona inda wasu mutane da ba’asan ko suwaye ba suka bi shi suka kashe shi.

Haushin an kashe musu daya daga cikinsu yasa suka bazama kan titi inda suka tsare matafiya dake tafiya Abuja da kuma masu shiga Kaduna.

Hakan ya haifar da cinkoson ababen hawa a hanyar.

Matasan wadanda suka koka kan rashin tsaro a kauyen sun ce baza su bar hanyar ba har sai gwamnati ta tabbatar da zata samar musu da tsaro a kauyen nasu.

You may also like