Matasa sun babbake gidan Sanata Sha’aba Lafiagi na jihar Kwara, a jajiberen zaben kananan hukumomi.
Wani ganau ya bayyanawa manema labarai cewa, lamarin ya faru ne yayin da sojojin da ke tare da Sanatan suka budewa fararen hula wuta. Wanda hakan ya jikkata wasu, yayin da wasu kuma suka arce.
Wannan ne ya hasala matasan suka banka wa gidan Sanatan wuta.