Wasu matasa a Babban birnin jihar Neja wato, Minna sun sake gudanar da tarzoma na nuna rashin Jin dadinsu ga kamfanin raba hasken wutar lantarki ta AEDC kan yadda ake fuskantar karancin wutar lantarki a jihar
Tun a watan Oktoba ne, dai matasa suka kamfanin wa’adi kan idan har ba zai iya samar da wadataccen hasken wutar lantarki ba, to ya fice daga jihar. Matasan dai sun nuna cewa duk da cewa manyan tasoshin samar da wutar lantarki na Shiroro da Kainji duk a cikin jihar suke amma kuma jihohin makwaftaka sun fi samun wutar lantarkin.