Matasan Arewa na shirin sassauta wa’adin da su ka ba Igbo


Kungiyar Matasan Arewa tare da hadin kan sauran kungiyoyin Arewa su na shirin sake yin nazarin wannan matsayin da su ka dauka na korar kabilar Igbo daga Arewa.

Kungiyar dai ta bai wa dukkan wani dan kabilar Igbo wa’adin wata uku da ya fice daga Arewa.

Kodinatan kungiyar Yerima Shettima ne ya nuna yiwuwar sake yin nazarin ganin yadda gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas da sauran kungiyoyin yankin irin su Ohanaeze Ndigbo su ka nesanta kan su da masu kiran Inyamurai su balle su kafa Biafra.

“Ko dama tun da farko a baya ai ba wani abu ba ne ya sa mu ka bada wancan wa’adin sai ganin yadda gwamnonin yankin Kudu masu Gabas su ka yi gum da bakin su, ba su nesanta kan su da masu neman kafa Biafra ba. Inji Shettima.

Ya kara da cewa har yanzu dai ba su cimma wata matsaya ba, amma dai ya ce nan ba da dadewa ba za su sake zama domin su sake nazarin wannan wa’adi da su ka bayar.

You may also like