Matasan Daura za su sayawa Buhari Fom ɗin takara 


Wata kungiyar matasan masarautar Daura mai suna Daura Emirate Youth Progressive Movement (DEYPM) ta yi alkawarin sayawa shugaban kasa Muhammad Buhari fam ɗin tsayawa takara a shekarar 2019.

Kungiyar ta  kuma ce zata sayawa gwamna Aminu Bello Masari fom na tsayawa takara a shekarar 2019.

Abdulkadir Lawal, shugaban kungiyar shine ya bayyana haka yayin wani taron gangami da aka gudanar a Katsina.

Taran gangamin ya samu halartar dubban matasa da suka fito daga kananan hukumomi biyar dake ƙarƙashin masarautar Daura.

“Zamu sai musu fom ɗin  a matsayin gudunmawarmu na goyon bayan jagororin siyasar biyu kan su sake tsayawa takara a karo na biyu a zabe,” ya ce.

Ya ce kungiyar ta yanke shawarar sayawa Buhari da Masari fom saboda kwazon da suka nuna.

Lawal yace Shugabannin biyu sun kawo cigaba cikin sauri a wuraren da suke jagoranci  musamman bangaren tsaro, aikin noma da sauransu.
“Gwamna Masari ya samu nasara wajen bunkasa ilimi, kiwon lafiya abubuwan more rayuwa a jihar cikin shekara biyu da yayi,”

You may also like