Wasu masu matasan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zangar neman a cire shugaban jam’iyyar APC John Odigie Oyegun daga mukaminsa.
Masu zanga-zangar da suka mamaye hedikwatar jam’iyar a ranar Litinin dauke da kwalaye da aka rubuta: ‘a cire Onyegun yanzu’, ‘ a daina saba kundin tsarin mulkin jam’iyya’ da sauransu.
Onyegun wanda aka hango shi yana shiga sakatariyar jam’iyar ba tare da ya damu da masu zanga-zangar ba.
Da yake magana da manema labarai ranar Litinin, Peter Oyewole shugaban masu zanga-zangar ya ce idan ba a cire Onyegun ba to zai ci gaba da jawo wa shugaban kasa Buhari bakin jini.
Oyewole ya ce matsayin cin hanci da kuma yadda ake kababa yan takara a matakai daban daban-daban abune mai tsoratarwa.
” Tun shekarar 2015, ba a taba bayyana wa jama’a kasafin kudin jam’iyar APC ba, tun shakerar 2015 jam’iyar APC bata taɓa gudanar da wani babban taro ba. Wadannan kwararan hujjoji da za su sa a cire shugaban jam’iyya. Muna bukatar a cire Oyegun yanzu.”
Karshe masu zanga-zangar sun yi barazanar cewa in har ba a cire Oyegun ba cikin wata guda to za su mamaye sakatariyar jam’iyar su kuma hana kowa shiga.