Matasan Yankin Arewa Ta Tsakiya Sun Bukaci Buhari Ya Fito Takara A 2019


Wasu matasa da suka fito daga yankin arewa ta tsakiya sun yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya nemi takara karo na biyu a zaben shekarar 2019.

Matasan karkashin kungiyar Shugabannin kungiyoyin matasan arewa ta tsakiya sun yi wannan kiran ne a minna cikin sanarwar bayan taro da suka fitar.

Sanarwar dake ɗauke da sahannun Alfa Nma, jami’in tsare-tsare na kasa, Nuruddeen Iliya, sakatare da kuma Zara Musa shugaba, tace kungiyar zata shiga tattaunawa da wasu fitattun yan Najeriya domin su shawo kan shugaba Buhari ya tsaya takara a shekarar 2019.

Kungiyar tace kiran na shugaban ƙasar ya tsaya takara ya zama wajibi duba da irin cigaban da ya samar a yankin dama Najeriya baki daya.

” Bayan duba na tsanaki kan aikace-aikacen gwamnatin shugaba Buhari da kuma sauyin da ta kawo a yankin arewa ta tsakiya mun yanke shawarar cewa Buhari ya nemi takara a 2019.

“Ga baki dayan matasan yankin arewa ta tsakiya a shirye suke su mara masa baya ta wannan fanni,” sanarwar tace.

Sanarwar ta kara da cewa Buhari yana bukatar zango na biyu domin cigaba da yaki da cin hanci da rashawa da yake.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like