Matashi Ya Auri Mata Biyu A Lokaci GudaWani matashi mai suna Isiyaku Dahiru, wanda ya kammala karatu a fannin akawun a makarantar ‘Federal Polytechnic dake jihar Nasarawa, ya auri mata biyu a rana guda.
Kara mata biyu a lokaci guda da Isiyaku ya yi ya sanya matansa uku a yanzu. An daura auren ne a ranar Asabar din da ta gabata.
Angon ya soma sanya hotunansa da ‘yan matan da ya auran ne wato Khadija da Rashida a shafinsa na ‘facebook.’
An daura auren farko ne a da misalin karfe goma na safe RCM School’ dake garin Doma a jihar Nassarawa, daga bisani kuma bayan kimanin awa guda aka garzaya kan layin Sakora Dakashi dake kan titi Lafiya a garin Doma shi ma a jihar Nassarawa domin daura aure na biyun.
Yanzu haka ango da amaren sun tare a gidan su dake kan titin Lafiya a garin Doma jihar Nassarawa.

You may also like