
Asalin hoton, OTHER
Beatrice da Sonia Ekweremadu a wajen kotu a Birtaniya
Kotu ta samu Sanata Ike Ikweremadu da matarsa Beatrice da laifin yunƙurin cire ƙodar wani saurayi talaka, ta hanyar kai shi London domin ya bayar da ƙodar.
BBC ta binciko yadda lamarin ya faru, yayin da suke jiran a yanke masu hukunci.
Sonia Ekweremadu, wadda ɗaliba a ɗaya daga cikin jami’o’i mafiya shahara a Birtaniya, ta fito ne daga gidan masu hali, kuma ɗaya daga cikin manyan ƴan siyasa a Najeriya,
To amma tana fama da rashin lafiya, kuma tana matuƙar buƙatar wanda zai ba ta ƙoda.
Mahaifinta, Ekweremadu ya biya dillalai dubban kuɗaɗen Birtaniya domin samo wanda zai bayar da gudummawar ƙodar.
Daniel, wanda ba za mu bayyana sunansa ba, ya taso ne a wani iyali mai girma da ke rayuwa a wani ƙauye a Najeriya, inda babu ruwan famfo kuma babu lantarki.
Yana da shekara 15, kuma yana sana’ar sayar da kayan wayar hannu a cikin baro, a birnin Legas, inda yake tura wa iyayensa ɗan abin da ya samu.
A 2022, lokacin yana da shekara 21, ya shiga wani ofishin ƴan sanda da ke kusa da Heathrow, a gajiye, cikin tashin hankali.
Ya shaida wa ƴan sanda cewar ya tsere ne bayan da wasu mutane suka yi yunƙurin cire ɗaya daga cikin ƙodarsa.
A ɗaya ɓangaren kuwa, yayin da Daniel ke tura baro, Ike Ikweremadu da matarsa Beatrice na cikin tashin hankali kan rashin lafiyar ƴarsu Beatrice, wadda za ta iya rasa ranta.
Iyalin Ikweremadu sun tunkari wani mutum mai suna Dr Obinna Obeta, wanda shi ma ya samu gudumawar ƙoda a 2021, wanda aka yi masa aiki a asibitin Royal Cambridge Hospital.
Asalin hoton, SOCIAL MEDIA
Ike Ekweremadu
Iyalan Ikweremadu sun so ne Dr Obeta ya sake kwatanta abin da ya faru da shi a kan ƴarsu Sonia
Daga nan ne Dr Obeta ya buƙaci wanda ya ba shi gudumawar tasa kodar da ya binciko wanda zai bai wa Sonia gudummawar tasa ƙodar.
Inda aka bayar da sunan Daniel.
Daniel ya bayyana cewa Dr Obeta ya yi alkawarin kai shi Landan amma bai faɗa masa cewar za a cire masa ƙoda ba.
Daniel ya ce wa kotu “Na zaci cewa zan zauna gidansa ne kuma zai nema min aiki. Ya ce min kada na faɗa wa kowa cewa zan je Birtaniya.”
Daniel ya zaci a kan batun takardar shiga Birtaniya ne, lokacin da Dr Obeta ya ce masa zai yi gwaje-gwaje a asibiti.
An ba Daniel takardar shiga Birtnayi ne a watan Janairun 2022.
Daniel ya ce na zaci taimakona zai yi.
Sai dai ya ce a lokacin da suka isa Landan ya zama tamkar ɗan aiki a gidan Dr Obeta.
Ta bayan fage kuwa Ike Ekweremadu na samun bayani daga wani ɗan uwansa, wanda shi ma likita ne, wanda aka umurce shi ya biya Dr Obeta kuɗi kimanin fan 2,000.
Shi kuwa Daniel an shirya cewa za a ba shi fan 6,000 kan ƙodar tasa, yayin da aikin musayar ƙodar za a yi shi a ɓangaren masu hannu da shuni na asibitin Royal Free da ke London kan kuɗi fan 80,000.
A Birtaniya laifi ne a biya wanda zai bayar da gudmawar wata gaɓa tashi, waɗanda yawanci ƴan uwa ne na kusa.
Da alama Ekweremadu da iyalansa sun san da wannan doka.
Sun gayyaci Daniel domin cin abinci a wani gidan cin abinci na mutanen Yammacin Afirka da ke London, kuma an buƙace shi ya sanya kaya masu kyau.
Sonia ma ta halarci wurin cin abincin har ma an ɗauki hotonta tare da Daniel.
Kotu ta wanke Sonia daga zargin hannu a cikin lamarin.
Asalin hoton, METROPOLITAN POLICE
Sonia Ekweremadu tare da Daniel
A ranar 22 ga watan Fabarairun 2022 ne Daniel da Sonia da kuma babban likitan ƙoda Dr Peter Dupont suka haɗu a karon farko.
Daniel ya shaida wa kotu cewa: “Ya tambaye ni, cewa, ko na san cewar zan bayar da ƙodata. Na kaɗu. A ranar ne na fara jin wani abu wai shi dashen ƙoda.”
Ya ƙara da cewa a ranar ne ya fara jin sunan Ekweremadu: “Ina ta kuka, jikina na rawa.”
A wata takarda da ya rubuta yana neman shawara daga abokin aikinsa, Dr Dupont ya fadi cewa Daniel bai taɓa haɗuwa da Sonia, wadda aka yi iƙirarin cewa ƴar uwarsa ba ce sai a ranar.
Sannan likitan ya ce hankalinsa bai kwanta da maganar ba.
Wani likitan na biyu da aka kawo domin aikin, Dr Philip Masson, shi ma hankalinsa bai kwanta da lamarin ba kasancewar ya lura cewa Daniel bai fahimci haɗarin bayar da gudummawar ƙoda ba.
Daga nan ne Dr Dupont ya dakatar da batun dashen ƙodar, inda ya ce Daniel ba zai iya bayar da ƙodar ba kuma ba ya da alaƙa mai ƙarfi da wadda za a bai wa gudumawar ƙodar.
Sannan ba zai iya ɗaukar nauyin ci gaba da kula da lafiyarsa ba bayan aikin.
Asalin hoton, INSTAGRAM
Sonia Ekweremadu na matuƙar buƙatar gudummawar ƙoda
A cikin makonni bayan haka, Ike Ikweremadu ya rinƙa tura wa Sonia hotunan waɗanda ake tunanin za su iya bayar da gudummawar ƙodar.
An ga yadda take ba shi amsa, tana cewa: “Wannan baƙin zai fi. Wannan farin da alama zai iya guduwa.”
A ɓangare ɗaya kuma wasu mutane biyu sun ziyarci Daniel a gidan Dr Obeta da ke kudancin birnin London.
Wani likita daga cikinsu ya danna cikin Daniel, abin da ya sanya hankalin Daniel ya tashi, ya yi tunanin cewa kila za su yi ƙoƙarin cire ƙodar ta hanyar tilasta masa da zarar ya koma Najeriya.
Daga nan ne ya garzaya wurin ƴansanda, inda aka samu nasarar kama Ekweremadu, da matarsa Beatrice da kuma ɗiyarsu Sonia, tare da Dr Obeta.
Yanzu an samu mutanen uku da laifin karya dokar hana bauta ta hanyar kai Daniel Birtanyia domin samar da ƙodar da za a sanya wa Sonia.