Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Matashiya mai lalurar gani da ke sana’ar girke-girken zamani
Duk da lalurar da take da aka haife ta da ita ta rashin gani, wannan bai hana ta ƙoƙarin cimma burinta ba.
A baya-bayan nan Halima Jibril Usman ta ja hankalin al’umma bayan da ta fara wallafa hotunan aikin da take gudanarwa a shafukan sada zumunta.
Duk da cewa akwai maza da mata da dama da ke sana’ar girke-girke kuma suke wallafawa a shafukan sada zumunta, lamarin Halima ya ja hankali ne kasancewar tana fama da lalurar gani.
Al’amari ne mai sammatsi, to amma da alama Halima ta shawo kan wannan ƙalubale, har ma ta zarce wasu da dama a wannan ɓangare.
Wace ce Halima Jibril?
Asalin hoton, Instagram/the_blind_kitchen_creations
An haifi Halima a birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya, kuma tun asali an haife ta ne da lalurar rashin gani.
Ta fara karatu a jihar Kaduna, kafin daga baya ta koma Abuja, inda tra ci gaba da karatu a makarantar masu lalurar rashin gani.
Yanzu kuma tana karatu a jami’ar jihar Kaduna.
Yaushe ta fara koyon girki?
Halima ta ce ta fara koyon girki ne tun tana ƙarama.
Ta ce “na fara koyon girki tun ina shekara tara ko goma.”
Ta ce duk da cewa tana da matuƙar ƙaunar girki, amma mahaifiyarta ta taka muhimmiyar rawa wajen ƙwarewarta a harkar girki.