Matata Tana Dukana A Duk Lokacin Da Taga Dama,Wani mutum ya shaidawa Kotu


Hakkin mallakar Hoto:Daily Trust

Wani ma’akaci da yayi ritaya Taofeek Giwa ya roki kotun gargajiya ta  Idi-Ogungun  dake Ibadan kan taraba aurensa da matarsa Abiodun Omotayo,kan cewa tana dukansa a duk lokacin da taga dama. 

Giwa wanda bai dade da barin aiki da hukumar kula da gidan yari ta kasa ba, ya shigar da kara a ranar 9 ga watan Yuni,Yana bukatar kotun da ta raba aurensu da suka shafe shekara 7 tare. 

A cewar Giwa matar tana amfani da girman jiki da tafi shi wajen takura masa. 

” Tana dukana kan sabani kadan, bazan iya yimata gyara ba idan tayi kuskure, a takaice ma dai yana daga cikin dabi’arta ta yaga min riga, “yace. 

” Ya mai Shari’a abu mafi muni da tayi shine na saka mini guba a abinci domin naci na mutu,kuma ni ban shirya mutuwa yanzu ba. 

 ” Ina rokon kotu da ta raba auren mu saboda akareni daga mutuwa da wuri domin na  kula da yayana,”Yace. 

Da take kare kanta Omotayo ta musalta dukkanin zargin da ake mata amma ta fadawa kotun cewa mai karar shine yake binta da adda zai yankata. 

Ta yarda da bukatar da ya shigar kan rabuwar auren, inda tace ta gaji da zama da mai karar saboda rayuwarsa ta neman mata da yake.

Amma ta roki kotun da ta bata damar  rikon da daya da suka haifa domin ya samu kulawa. 

Shugaban kotun Mukaila Balogun,ya raba auren ya kuma bata rikon yaron. 

Amma ya umarci mai kara da ya rika biyan naira 3000 kudin kula da yaron. 

You may also like