Ministan Mai na Kasar Nijar, Mista Foumakoye Gado ya tattauna da Shugaban Kamfanin Mai Na Kasa( NNPC), Maikanti Baro bisa shirye shiryen fara shigo da danyen mai daga Nijiar don tace shi a matatan mai na Kaduna sakamakon hare hare da tsagerun Niger Delta ke kaiwa kan bututun mai.
A kwanan nan ne dai, matatan mai na Kaduna ya fara aiki amma kuma ana fuskantar karancin danyen mai sakamakon ayyukan tsagerun Niger Delta. Haka nan kuma kamfanin NNPC zai shinfida bututun mai daga Kaduna zuwa garin Agadem na kasar Nijar don samun danyen mai cikin sauki.