Matatun man Nijieriya guda uku da suka fara aiki kwanan nan sun tace lita sama da milyan hudu na kananzir ba ya ga lita fiye da goma sha biyu na man Diesel da suka samu nasarar tacewa.
Jami’in da ke kula da matatun, Mista Anibor Kragar ya tabbatar da cewa a halin yanzu matatun man suna aiki gadan gadan inda ya kara cewa nan bada jimawa matatun za su fara samar da man da jiragen sama ke amfani da su.