Mayu da masu sihiri tare da mabiyansu a kasar Amurka sun tayar wa shugaban kasar su Donald Trump da nufin sai an tsige shi daga kan mukamin shugabancin kasar.
Wannan na zuwa ne a lokacin da galibi a cikin ‘yan adawar gwamnatin nasa na ganin hakan ba mai iya faruwa bace.
Da tsakar daren Juma’ar da ta gabata, Mayun da mabiyansu a sassa daban-daban na Amurka sun yi wani taron tsinuwa na musamman ga shugaba Trump.
Haka kuma sun shirya gudanar da tarukan tsinuwar a ranakun da farin wata ya wuce rabi, har sai Trump ya bar ofishin shugabancin Amurka.
Masihirtan sun ce burinsu shi ne su makantar da Trump domin kada ya iya aiwatar da miyagun manufofin da ya kudirta, su kuma hana shi rarraba kawunan al’ummar kasar, da tauye ‘yanci da cusa kiyayya a zukatan mutane. Haka kuma su na da niyyar daure harshen duk magoya bayansa da zummar hana su magana.
“A karkashin sharudan maita a Amurka, ba a ‘makantarwa’ da nufin cutar da mutumin da aka yi dominsa, illa domin hana shi cutar da sauran mutane. Masu ra’ayin maitar sun ce sun dauki matakin taka wa Trump birki ne domin jin dadin illahirin jama’a”, kamar yadda rahotan BBC ya bayyana.
Toh sai dai shi kansa wannan al’amari ya kawo rabuwar kawunan mutanen kasar Amurka, domin kuwa wata kungiyar kiristocin kasar ta yi tur da al’amarin.
Kungiyar mai suna “Christian Nationalist Alliance” mai ra’ayin rikau da kishin kasa ita ma ta gudanar da taron addu’o’i a ranar 24 ga Faburairu domin kalubalantar tsubbate-tsubbaten mayun.
Tuni dai shafin Facebook da aka bude na Mayun domin gudanar da sihirce sihircen su ya samu mabiya fiye da 10,000, inda har sun kirkiro wani sabon maudu’in intanet mai suna #magicresistance.
Izuwa yanzu Trump bai ce uffan ba game da wannan al’amari.