Matsalar isar da agaji ga mabukatan Siriya


 

 

 

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Bashar al-Assad ta bada damar shigo da kayan abinci da magunguna ga yankunan da ‘yan tawaye ke iko da su

Syrien Aleppo Humanitäre Hilfe

Yanzu haka dai dimbin mata da kananan yara da ke galabaice a birnin Aleppo suna matukar jiran agajin gaggawa. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da aka tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta, tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar ta Siriya zuwa sa’o’i 48 da kasashen Rasha da Amirka suka sake cimma.

Majalisar Dinklin Duniya ta ce a yanzu dai ana kwana na biyu kenan da motocin dakon kaya makare da abinci ke makale a kan iyakar kasashen Turkiya da Siriya, wanda suke fatan kayan su iso ga yankunan da ‘yan tawayen suka killace a birnin Aleppo nan ba da jimawa ba. To sai dai akwai fargabar matsalar ka iya shafar dubban fararen hula da ke fama da yunwa a karkashin ikon ‘yan tawaye, ko da yake shugaban Siriya Bashar al-Assad ya sha alwashin kwace dukkanin yankunan da ke hannun ‘yan tawaye, gabannin sanya hannu a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma wanda ta fara aiki a wannan mako.

You may also like