Jami’an kamfanin mai na kasa (NNPC) tare da hadin guiwar jami’an tsaro sun gano wani depot inda aka boye fetur a cikin Babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban Kamfanin NNPC, Baru Maikanti ya nuna bakin cikinsa kan yadda wadanda suka mallaki depot din suka boye fetur alhali suna kallon yadda magidanta ke kwana gidajen mai don saye fetur da za su yi tafiya garuruwansu don bikin Kirismeti.