Shugaban kasa Muhammad Buhari wanda a yanzu haka ke ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Kano ya ce Najeriya ita ce matsalarsa.
Buhari ya bayyana haka a wurin taron cin abincin dare da gwamnatin Kano ta shirya masa a ranar Laraba.
Yayi alƙawarin ci gaba da tsayawa tsayin daka domin farfaɗo da kimar kasarnan.
Buhari yace gwamnatinsa za ta cigaba da bawa fannin ilimi muhimmanci domin gina matasa ta yadda suma za su bada gudunmawrsu ga cigaban kasa.
“Najeriya ce matsala,” ya ce.
“Zan cigaba da yin iya kokarina. Zan tsaya tsayin daka domin ciyar da ƙasarnan gaba.”