Matsalar yunwa ta ritsa da yara masu yawa a Najeriya


Wannan sabon bayani da asusun na Unicef ya fitar ya nuna cewa yara kanana da ke fuskantar barazana na rashin abinci mai gina jiki da tuni matsalar ta tamowa ta adabe su a yankin arewa maso gabas na karuwa.

19421159_303

 

Assusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar damuwa a kan karuwar yawan yara kanana da ke fuskantara barazanar karancin abinci mai gina jiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya da yawansu ya kai dubu 400. Abin da ya sanya kwararru gargadin mumunar illar da ke fuskantar wadannan yara.

Nigeria Ärzte ohne Grenzen in Borno (MSF/C. Magone)

Karuwar kyautatuwar yanayin tsaro ya bai wa jami’an asusun kula da lafiyar yara kanana na Majalisar Dinkin Duniyar uzurin kai wa ga wasu yankuna inda ake gano yaran da ke fuskantar wannan matsala, abin da kwarrau a fannin kula da lafiya suka bayyana damuwa a kan illa da suka kira ta har abada da ka iya kama yaran. Dr Mairo Mandara ita ce shugabar gidauniyar Bill and Melinda a Najeriya ta bayyana cewa haka zai iya taba yanayin da yaran za su kasance har abada.

Nigeria Armee rettet Mädchen (picture-alliance/dpa/EPA/Nigerian Army)

Kyautatuwar yanayin tsaro dai ya sanya samun Karin yara kanana da ke fuskantar matsalar ta tamowa, domin kuwa asusun na Unicef ya ce yanzu yana iya kai wa ga mutane 750,000 a dai dai lokacin da yake fuskantar karancin kudadden  kai tallafin da ya sanya shi sauya adadin daga dalla milyan 55 zuwa dalla milyan 155. Ko me hukumomi ke yi a kan wannan. Sanata Baba Kaka Bashir wakili ne daga jihar Borno inda aka fi fama da matsalar, wanda ya ce matsalar tsaro ta gama tagaiyara mutanen yankin.

Duk da taimako na bilyoyin da aka samu a bayyane take a fili cewa sai ‘yan Najeriya sun taimaki gwamnati da kungiyoyin kasa da kasa domin ceto yarara kanana daga matsalar karancin abinci mai gina jiki domin samun makoma mai kyau.

You may also like