
An riƙa fuskantar tashin-tashina a wasu jihohi wanda fafatawar ta yi zafi a cikinsu.
Tashin hankali da rikici da barazana ga masu zaɓe na daga cikin abubuwan da suka mamaye zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jihohi da aka yi a jihohi 28 cikin 36 da Najeriya ke da su a ranar 18 ga watan Maris na 2023.
Tun da fari an tsara gudanar da zaɓen a ranar 11 ga watan Maris amma an sauya hakan bayan ƙarar da jam’iyyun adawa suka shigar na ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu.
An fara zaɓen kan lokaci a wasu sassan ƙasar, ba kamar yadda aka yi ba a zaɓen shugaban ƙasa da ba a fara zaɓen ba ma a wasu sassan har sai da lokacin da aka tsara farawar ya wuce.
Rikici da hana masu zaɓe fitowa
A Kano, inda nan ne cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya, wani wakilin BBC ya shaida yadda ‘yan daba suka rika kai hare-hare rumfunan zaɓe.
A dai jihar ‘yan sanda sun kama shugaban hukumar sufuri da laifin jagorantar ‘yan daba su tayar da hayaniya a wurin zaɓe.
Ka zalika ‘yan sanda sun kama gwamman mutane da aka zarga da shirin tayar da hankali a yayin zaɓen.
A Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers mai arziƙin mai, wani wakilin na BBC ya naɗi wani bidiyo na bayan harin da aka kai wa wata rumfar zaɓe inda aka ƙona takardun zaɓe.
Waɗanda suka shaida lamarin sun zargi ‘yan daban jam’iyyar da ke mulki a jihar ta PDP da kitsa hakan.
“Na rantse ba zan ƙara yin zaɓe ba,” in ji wani da aka hana kaɗa ƙuri’arsa.
“Mun ɓata lokacinmu don muzo mu yi zaɓe, in ji wani shi ma, ya ƙara da cewa ‘yan daban da ke yi wa PDP aiki sun ƙwace akwatin zaɓen, sun ƙona takardun. Sai dai BBC ba ta tabbatar da iƙirarin nasa ba.
A dai Rivers din an kashe wani mutum da aka ce shugaban yaƙin neman zaɓe ne a ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma a ranar zaɓen.
A cewar jam’iyyar an kashe mutumin ne lokacin da yake ƙoƙarin hana ‘yan daba kwashe kayan zaɓen.
Kungiyar cibiyar haɓɓaka dimokradiyya da ta riƙa bibiyar zaɓen ta bayyana cewa an riƙa hana mutane zaɓe a jihohin Bayelsa da Enugu da Jigawa da Sokoto da kuma Legas.
Jami’an da suka yi wa BBC aiki a Abia da Enugu sun shaida yadda ‘yan daba suka kai hare-hare kan rumfunan zaɓe.
A Abia, Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar INEC ta bayar da rahoton yadda ‘yan banga suka kai wa cibiyar tattara bayanan zaɓenta hari a birnin Umuahia.
“Suna son karɓe mana ƙasa”
Babu abin da ya mamaye tattaunawar da aka riƙa yi gabanin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha a Legas sai maganar barazana da hana masu zaɓe kaɗa kuri’a, sakamakon irin waɗannan abubuwan da suka faru a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda wani shugaban kungiyar masu sufuri yake faɗawa waɗanda ba za su zaɓi APC ba cewa su zauna a gida cikin fushi.
Sai dai mutumin da ake kira Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da Mc Oluomo, ya ce bidiyon da aka ɗauke shi a manhajar Instagram kai tsaye yana maganar wani abu ne mai kama da “nishadi”.
Jami’an tsaro a bakin aiki a jehar Legas inda APC ta lashe zaɓe
An yi ta kiraye-kirayen cewa ‘yan sanda su kama Mista Akinsanya, sai dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas Idowu Owohunwa cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce za su ɗauki maganar a matsayin nishadi, amma za su yi bincike.
Bayanai kan barazana da hana masu zaɓe kaɗa ƙuri’a sun ƙara zama ruwan dare ne a ranar zaɓe yayin da aka riƙa ganin wasu hotunan bidiyo na wasu da aka yi amannar ‘yan APC ne suna yawo a kan titunan Legas suna cewa duk wanda ba zai zaɓi APC ba ya koma gida.
BBC ta binciki wani bidiyo da aka gano an naɗa ne a unguwar Mafoluku da ke yanin Oshodi a jihar ta Legas.
A wani bidiyo shi ma da BBC ta tabbatar a ranar 18 ga watan Maris, an ji gungun wasu mutane suna shaidawa waɗanda ba za su zaɓi APC ba su zauna a gida kada su sake su fito.
An ga irin waɗannan da dama a kafafen sada zumunta da mutane suka riƙa ɗauka.
Yadda aka yi watsi da takardun zaɓe a wasu sassan Najeriya
A legas, ɗan jaridar BBC ya ga lokacin da wasu ‘yan banga suka kai hari kan wata rumfar zaɓe, sun kwace takardun sun hana zaɓe a wasu rumfunan na daban a yankin Lekki da ke Legas.
Wakilin BBC wanda ya aike rahoto daga yankin Victoria Garden a Legas, inda aka dage zaɓen zuwa 19 ga watan Maris saboda rashin jituwa a wasu rumfunan zaɓe, an rawaito hatsaniya tsakanin magoya bayan LP da APC saboda rashin jami’an tsaro.
Bayo Onanuga wanda tsohon ma’aikacin kamfanin dillancin labarai na Najeriya ne NAN, kuma darakta ne na yaɗa labarai a yakin neman zaɓen Tinubu da Shettimma, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa zaɓen 2023, “zai zama zaɓe na ƙarshe da Igbo za su ƙara katsa landan a siyasar Legas”, abin da ya ja ake ta kiran cewa a sauke wannan saƙon da ya wallafa.
Saƙon na shi ya sake jaddada abin da wasu masu bayyana ra’ayinsu na kafafen sada zumunta ke cewa yana nuna goyon bayansa ne ga masu tayar da hankali kuma duk suna yin hakan ne a yankin da ƙabilar Igbo suke da matukar yawa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Igbo ne, Peter Obi.
LP ta kayar da jam’iyyar APC mai mulki a Legas yayin zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana, kuma mutane da dama sun yi amannar cewa dan takarar jam’iyyar na gwamna a jihar Gbadebo Rhodes-Vivour zai iya samun nasara kan wanda yake mulki Babajide Sanwo-Olu, sai dai daga baya kuma ya yi rashin nasara.