Matsalolin Tsaron Na Tasiri A Rashin Fahimtar Addini-Kwararru
Bisa ga bayanan kwararru, wasu daga cikin matsalolin tsaron na Najeriya na da nasaba da banbancin fahimtar addini. Dangane da haka ne, Cibiyar Interfaith Mediation Center dake aikin wanzar da zaman lafiya a tsakanin addinai, ta shirya taron tattaunawa a Kano tsakanin mabiya dariku daban-daban domin kara fahimtar juna.

An zabo mahalarta taron ne daga darikun Izala da Qadiryya da Tijjaniya da kuma Shi’a, wadanda suka hada maza da mata musamman matasa da malamai inda masana daga dukkanin bangarorin suka gabatar da makala da jawabai game da muhimmancin zaman lafiya a tsakanin juna duk kuwa da banbancin fahimtar su a sha’anin addini.

Taron ya gudana ne karkashin shirin gudunmawar al’uma a tsarin wanzar da zaman lafiya na Cibiyar Interfaith Mediation Center, wadda ke samun tallafi daga hukumar USAID ta kasar Amurka dake gudanar da ayyukan ci gaba a kasashen duniya.

A bayaninsa, Ahmad Tijjani Adam babban Jami’in aikace-aikacen cibiyar yace daga cikin yyukan sun a wanzar da za,man lafiya shine suka shirya taron tattaunawa tsakanin mabiya dariku a addinin musulinci domin a rinka gudanar da taron wa’azi da lacca ba tare da kalaman batanci ga juna ba.

Shi kuwa Jibrin Abdulrahman daya daga cikin samari mabiya darikar shi’a da suka halarci taron cewa yayi irin wannan taron ya yi dai-dai da wadda malaman su kan shirya a duk shekara, inda ake gayyato malamai daga dukkannin dariku ayi musayar fahimta kan lamuran da suka shafi addini.

A nasa bangaren, Dr Aminu Isma’il Sagagi guda cikin masu makala a wurin taron yace haduwa irin wannan zata yi tasiri akan aikace-aikacen mayakan Boko Haram da ‘yan fashin daji.

Kamar ‘yan uwan su maza, su-ma matan da suka halarci taron sun sha alwashin isar da sakonnin da suka ji, inda guda daga cikin su Malama Fatima Barau Maiwake ke cewa, matakin farko na isar da sakon shine ‘yaya da abokan zama a gida.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

You may also like