
Asalin hoton, Reuters
Akalla mutum 38 ne rahotanni ke cewa sun rasa rayukansu a dalilin wani yanayi na sanyi da iskar mai karfi da suke ci gaba da mamaye Amurka da Canada.
Jami’an gwamnati sun ce mutum 34 ne suka mutu a Amurka, inda yankin da lamarin yafi shafa shi ne birnin Buffalo da ke Jihar New York.
Mutum hudu kuma sun mutu a Canada yayin da wata motar bas ta kwanta a bisa wata hanyar da kankara ta lullube baki dayanta kusa da garin Merritt a lardin British Columbia da ke yammacin kasar.
Asalin hoton, EPA
An shafe kwanaki wannan yanayin na kara tabarbarewa, sai dai an fara mayar da lantarki a wasu yankuna bayan da turakan lantarkin suka daina aiki saboda tsinkewar wayoyi da tsanannin sanyi da tarin dusar kankara suka shafa.
Zuwa ranar Lahadi, kasa da mutum 200,000 ne ke da lantarki a gidajensu, idan aaka kwatanta da mutum miliyan 1.7 kafin bayyanar wannan iftila’in, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito.
An kuma soke sauka da tashin dubban iragen sama, matakin da ya hana iyalai masu yawa isa gida domin yin shagulgulan Kirsimeti da ‘yan uwansu.
Fiye da Amurkawa miliyan 55 ne wannan yanayi ya ke ci gaba da shafa.
Sannan wannan yanayin ya mamaye wani babban yanki wanda ya taso daga gabashin Canada har zuwa JIhar Texas ta kudancin kasar Amurka.
Jihar Montana da ke yammacin Amurka ce wannan yanayin na sanyi yafi shafa, har ta kai ga sanyin ya kai maki -45 na ma’aunin celsius.
A Canada kuwa, lardunan Ontario da Wuebec ne ke ci gaba da fuskantar matsanancin sanyi da iska mai karfi.