Matsayin Amurka A Yunkurin Juyin Mulki A Turkiyya


 

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi watsi da zargin da ake na cewa Amurka na da hannu a kokarin juyin mulkin da akayi a Turkiyya ranar Juma’a.

Alokacin da yake magana da gidan talabijin na CNN a jiya Lahadi, Kerry yace, “Rashin tunani ne ace Amurka na da hannu a juyin mulkin.”

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya zargi malamin nan Fethullah Gulen, wanda ke zaune yanzu haka a jihar Pennsylvania dake nan Amurka, da cewar ya na da hannu wajen ingiza wannan tashin hankalin, ya kuma bukaci da a mayar da malamin zuwa Turkiyya.

Erdogan, wanda ya rika ambaton kalmar “makirai” wadanda ya bayyana da cewa mutane ne masu son hargitsa Turkiyya, maganar da ke nuni da cewa yana hannunka mai sanda ne da kasar Amurka. Ranar Asabar din data gabata ne Ministan ayyuka Suleyman Soylu, ya zargi Washington da hannu a kokarin juyin mulkin.

Kerry ya kuma fadawa gidan talabijin na CNN cewa Turkiyya bata bukaci a mika mata Mallam Fethullah Gulen ba, ya kuma fadawa ministan harkokin wajen Turkiyya cewa su bukaci a mayar da malamin a hukumance, ya kuma ce Amurka bata kokarin kare kowa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like