Muhammad Gudaji Kazaure, dan majalisar wakilai ta tarayya na jam’iyar APC daga jihar Jigawa ya nesanta kansa da rahoton da aka bayar na shirin da majalisun kasa keyi na tsige shugaba Buhari.
Wani zaman gaggawa na hadin gwiwa da majalisun suka gudanar sun amince da gindaya wasu sharuda 12 da suke buƙatar shugaban kasa yasa baki a ciki ko kuma ya fuskanci fushin majalisun.
A wani taron manema labarai jim kadan bayan gindaya wa shugaban kasa sharudan, Kazaure ya ce ba zai kasance cikin wadanda suka cimma wancan kuduri ba.
“Babu wanda ya isa ya tsige shugaban kasa matukar muna raye wannan ranar za ayi yaki,” ya ce.
Ya ce akwai sanatoci da kuma yan majalisar wakilai da baza su goyi bayan wannan kudurin ba.
Dan majalisar ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari da ya shiga tsakani akan abubuwan da suke faruwa.