Mawaki Morell ya Haska A Bikin Al’adu A Abuja. 


Fasihin mawakin zamanin nan da ya yi saurin haskakawa a fadin kasar nan, Musa Akillah wanda aka fi sani da Morell, ya yi matukar haskawa a bikin bajekolin al’adu da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata a dakin taro na Conference Center dake Abuja.
Fasahar matashin a fannin waka ta sanya ya yi zarra a yankin Arewa da ma yammacin Afrika.
A bayyana yake cewa shi kadai ne mawaki daga yankin Arewancin kasar nan da yake hadaka da manyan mawakan da suka shahara a duniya. Wanda a sakamakon haka ne ya kasance daya daga cikin mawakan da suka gabatar da wasa a gangamin yaki da cutar kansa da aka gudanar a jihar Kebbi wanda uwargidan gwamnan jihar ta Kebbi, Dakta Zainab Atiku Bagudu jagoranta, inda wasansa ya ja hankalin mahalarta taron. Har ta kai ga an yi masa kyaututtuka.

Haka kuma yana daga cikin dimbin mawakan da aka gayyata a fadin kasar nan kama daga na Turanci da Hausa, da suka gabatar da wasanni a bikin al’adu da aka gudanar a Abuja, wanda ‘yar gidan shugaban kasa Zahra Buhari ta jagoranta. Inda ya yi wakarsa mai taken Amarya wadda har ta kai ga ita kanta Zahra Buharin ta yaba da salon wakarsa.
A yayin zantawa da’ Yan Jaridu bayan kammala bikin al’adun, Morell wanda dan asalin jihar Borno ne, ya mika godiyarsa ga Allah bisa gayyatarsa da aka yi a wannan bikin, kasancewar ba shi kadai ne mawaki daga yankin Arewa ba. Ya kuma godewa shugabar kungiyar su ta Arewa Creative Industry, Hajiya Halima Idris kan yadda take tallafa musu don ganin matasa masu fasaha irinsa da sauran masu sana’ar dogaro da kai sun cimma kudirorinsu.

You may also like