Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Ba Da Lambar Yabo Na Oscar
An zabi Temilade Openiyi, wacce aka fi sani da Tems, a jerin sunayen fitattun ‘yan wasan fina finai na lambar Yabo ta Oscars 2023, saboda gudunmawar da ta bayar a rubuta wakar da ake kira ‘Lift Me Up’, daya daga cikin wakokin sauti na  wani fitaccen silma na Marvel’ Black Panther: Wakanda Forever.

Yayin da take tattaunawa game da wakar, Tems ta ca ta samu wahayi ne daga mutanen da suke rayuwarta a da, amma yanzu sun mutu.

“Bayan na yi magana da Ryan kuma na ji yadda yake jagorantar fim ɗin da wakar, hakan ne ya sa na so in rubuta wakar da za ta bayyana duk mutanen da na rasa a rayuwata. Na yi tunanin yadda zan ji idan da zan iya rera musu waka a yanzu kuma in bayyana yadda nake kewar su,” in ji Tems. .

Yayin da wasu fina-finan Afirka da bai fi a kirga ba suka samu lambobin yabo a wannan gagarumin bikin, ba a samu wani kaso mai karfi daga Nahiyar Afirka ba. Ya zuwa yanzu, ‘yar Afirka daya ce kadai ta samu lambar yabo a matsayin ‘yar wasan kwaikwayo, wato Charlize Theron, wata ‘yar Afirka ta Kudu saboda rawar da ta taka a fim din Monster na 2003. Shekaru 10 bayan haka, Lupita Nyong’o ta ci kyautar Mafi kyawun Jaruma saboda rawar da ta taka a cikin fim din da ake kira “12 years a slave. “

A bana babu wasu fina-finan Afirka da suka sami wakilta a cikin mafi kyawun fina-finai na duniya. An kuma yi watsi da fim din Woman King, wani fim na rukunin jarumai mata zalla mai suna Agojie.Source link


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like