Max Air zai kwaso yan Najeriya 3184 daga ƙasar Libiya


Kamfanin jiragen sama na Max Air zai kwaso yan Najeriya 3,184 cikin su 5030 da ake sa ran za su dawo gida  daga ƙasar Libiya, wata sanarwa daga kamfanin na Max Air ta bayyana haka.

A cewar sanarwar mai dauke da sahannun mai magana da yawun kamfanin, Alhaji Ibrahim Dahiru kamfanin ya sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakaninsa da gwamnatin tarayya akan haka, kuma za a fara jigilar mutanen cikin yan kwanaki kaɗan masu zuwa.

Yace an sanya hannu a kwangilar ne tsakanin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA da kuma wakilin kamfanin na Max Air, Malam Shehu Wada a ƙarshen makon nan.

“Da wannan cigaban da aka samu ana sa ran Max Air zai kwaso yan Najeriya 3184 daga Libiya cikin sahu shida ta hanyar yin amfani da babban jirgin kamfanin kirar Boeing 747-400.”

You may also like