Mayaƙan Boko Haram Sun Kai Min Hari – BurutaiHafsan Rundunar sojojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Yusif Burutai ya bayyana yadda mayakan Boko Haram suka yi wa tawagar sa Kwanton-bauna a jihar Borno. “Ina cikin tawagar yayin da Boko Haram suka kawo mana farmaki. 


Maimakon mu ja da baya zuwa Maiduguri, sai Na ce A’a!  Wannan abin tare ya ritsa da mu, don haka ba zan koma ba. Tare za mu tunkare su don gamawa da su,” Inji Burutai. 

“Don haka muka kutsa tare da sojojin muka murkushe su. Mun rasa Sojoji biyu, sannan Birgediya-Janar daya ya samu rauni a baya. Mun kashe mayakan su 10 sannan mun kama guda 5”.

You may also like