Kamfanin Dillancin Labaru Na Nijeriya ya tabbatar da cewa mayakan Boko Haram sun kashe ma’aikatan Jin kai na kasa da kasa a yayin wani mummunan hari da suka kai garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa mayakan Boko haram din sun kai harin ne a jiya Alhamis da misalin Karfe bakwai na Yamma inda suka arce da wata Ma’aikaciyar jinya guda daya. Daga cikin ma’aikatan jinya da suka kashe har da likita guda.