Mayaƙan BokoHaram 17 sun Miƙa Wuya Tare Da Bayyana Dalilin Yin Hakan


Kimanin mayakan Boko Haram 17 ne suka mika wuya ga rundunar Sojan Nijeriya a jiya Litinin sakamakon alkawarin da Shugaba Buhari ya yi masu na yi masu afuwa.

Da yake gabatar da mayakan Boko Haram din, Shugaban Shirin Zaman Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ya ce, a halin yanzu sun samar da cibiyoyi inda duk wani dan Boko Haram da ya mika wuya zai tafi wurin.

Ya ce, shirin na samun nasara inda ya ce a yankin Monguno, kimanin mayakan Boko Haram 70 ne suka mika wuya sai yankin Bama inda wasu mayakan 60 suka mika wuya.

You may also like