Mayakan Alshabab sun kai hari kan sansanin Sojojin Tarayyar Afrika dake Somalia


Mayakan kungiyar Alshabab sun gwabza fada na tsawon a wanni da dakarun samar da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka, bayan sun tayar da bom a wata mota a gaban sansanin sojojin.

Yan sanda da kuma sojojin kasar ta Somalia da ma bangaren yan kungiyar duk sun tabbatar da faruwar lamarin .

Mayakan Alshabab sun kai hari kan sansanin dakarun samar da tsaro na kungiyar Tarayyar Afirka dake garin Bulamarer, dake da tazarar kilomita 135 ta arewa maso yammacin babban birnin kasar Mogadishu, wajen karfe 9 na dare a gogon kasar, wani mazaunin yankin ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Rueters.

Tun bayan da suka janye daga birnin Mogadishu  a shekarar 2011, kungiyar dake da alaka da alkaida ta rasa iko da yawancin biranen Somalia da kuma garuruwa.Amma ta cigaba da iko a yankuna dake wajen babban birnin.

Tun da fari yan ta’addar sun tasar da motocin kunar bakin wake biyu daya tashi daya daga cikin motocin sojojin Tarayyar Afrika da kuma ta sojojin Somalia.

“Sannan kuma mayakan kungiyar Alshabab suka fara harbi daga karakashin bishiyoyi yaki ne ba karami ba,” ya ce.

You may also like