Mayakan Boko Haram Sun Kashe Sojoji Da Dama A Najeriya


 

Sojojin Nigeria da dama ne suka rasa rayukansu a wani hari wanda mayakan boko Haram suka kai masa.

Shafin yanar gizo na labarai ta Jaridar alyaumussabe ta kasar masar ta bayana mayakan na boko haram sun kai harin ne a wani sansanin sojojin da ke arewa maso gabacin kasar wanda yake fama da tashe tashen hankula..

wata majiya ta bayyana cewa mayakan na boko haram sun kori wasu sojoji a yankin wadanda suka fada ruwa inda kimani 22 daga cikinsu suka rasa rayukansu. Kuma akwai yiyuwa yawan wadanda suka rasun ya karu don har yanzun a akwai wasu sijojin da suka bace ba’a ganosu ba.

Kakakin rundunar sojojin Nigeria Sani Kuka Sheka ya tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa sojoji 13 ne suka ji rauni amma akwai da yawa wadanda ba’a gansu ba.

You may also like