Mayakan Boko Haram sun sake kai hari a garin Tumour


wp-1473924637932.jpg

 

‘Yan kungiyar Boko haram sun sake kaiwa mutanen garin Tumour hari, inda aka bayyana cewa Sojojin Nijar dake sintiri a harabar garin na Tumour sun gwabza fada da mayakan na Boko Haram.

 

Wani mazaunin garin na Tumour da ya nemi a sakaye sunan sa, ya ce a lokacin da mayakan na Boko Haram suka sake kutsawa garin na Tumour, sun kama Filani guda uku inda suka umurce su, da su nuna musu gawarwarkin mayakansu da aka kashe.

Sai dai mayakan basu samu nasarar daukar gawarwakin ‘yan uwansu ba jami’an soji suka yi musu dirar mikiya, aka cigaba da musayar wuta kafin daga bisani sojojin su samu nasarar korar mayakan.

Mazaunin garin ya ce yawan ‘yan Boko Haram din da suka kutsa garin, sun kai 100 akan dawakai da rakuma.

Game da halin da ake ciki kuwa a garin na Tumour, mazaunin ya ce mutane suna zaune cikin gidajensu, in banda ‘yan sintiri na sa kai da ke zagaya garin dauke da kwari da baka, sai kuma sauran jami’an tsaro da ke sintiri.

You may also like