Mayakan BokoHaram 1000 Sun Yi Saranda


Mayakan Boko Haram fiye da 1000, ‘yan asalin kasar Chadi da suka je Najeriya domin yi wa kungiyar yaki sun koma kasarsu tare da mika wuya ga hukumomi.

Wani jami’in kasar, Dimouya Souapepe, ne ya shaida wa BBC cewa, cikin mayakan har da mata da yara, kuma sun mika wuya ne ga jami’an tsaro tun watanni biyu da suka gabata.
Jami’in ya kara da cewa, ba wai ana tsare da su ba ne, amma za a sake su zuwa ga ‘yan uwansu bayan an kammala bincike a kansu.

A wani bangaren kuma babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai, ya ce kashi 60 cikin dari na mayakan Boko Haram ba daga Najeriya suke ba.
Kafar yada labarai ta AllAfrica ta bayar da rahoton cewa, Laftanar Janar Buratai ya yi bayanin haka ne a wata tattaunawa da suka yi da jami’in Majalisar Dinkin Duniya a Maiduguri, Mohammed Ibn Chambas.
Kungiyar Boko Haram dai ta yi barna sosai a yankin kudu da sahara, inda ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, kuma ta kwace iko da yankunan arewa maso gabashin Najeriya, da ma wasu yankuna a kasashen da ke makwabtaka.
A halin da ake ciki yanzu dai kungiyar ta rasa iko da yankuna da dama a bana, sakamakon taron dangi na sojojin kasashen yankin tafkin Chadi da ke makwabtaka da Najeriya..

You may also like