Akalla sojojin gwamnatin kasar Colombia hudu sun rasa rayukansu, a wani fadan da ya barke tsakaninsu da mayakansu sunkuru kungiyar nan ta FARC masu sukar lamirin gwamnati.
Ma’aikatar tsaro a Colombiar ta ce fadan ya barke ne kwana guda da kafin fara taro a tsakanin bangarorin biyu da nufin tsara hanyoyin fahimtar juna da ma tsagaita kai wajuna hare-hare.
Sabon rikicin ya barke ne a yankin Narino mai iyaka da kasar Ecuador a inda ake noma sinadarin Coca da ake hada hodar iblis da shi.
Mayakan na kungiyar FARC din dai na kan gaba wajen samun amfanio daga odar iblis, kayan mayen da Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar ta Colombia ce cibiyar samar da ita a duniyar.