Mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabab na kasar Somaliya sun mamaye wani gari mai muhimmanci bayan janyewar sojojin kasar Habasha daga garin.
Majiyar tsaron Somaliya a ta bakin Muhammad Nur Adan daya daga cikin jami’an tsaron kasar a garin Beledweyne ta sanar da cewa: Mayakan kungiyar ta’addanci ta Al-Shabab sun mamaye garin Halgan da ke tsakiyar kasar bayan janyewar sojojin kasar Habasha daga garin.
Garin Halgan shi ne gari na uku da sojojin Habasha suka fice daga ciki a kasar Somaliya a karkashin shirin gwamnatin Habasha na janye sojojinta daga Somaliya bayan kammala wa’adin aikinsu na wanzar da zaman lafiya a kasar karkashin jagorancin dakarun kungiyar tarayyar Afrika na “AMISON”.
A kasa da mako guda sojojin Habasha sun janye daga garuruwan Moqokori da El-Ali gami da garin na Halgan. Kasar Habasha dai tana da sojoji 4,400 da suke taimakawa sojojin gwamnatin Somaliya a fagen yaki da mayakan kungiyar Al-Shabab a kasar.