Mayakan IS sun janye daga birnin Palmyra


 

 

Mayakan IS sun janye daga garin Palmyra da asubahin ranar Lahadi, sakamakon zafafan hare-hare ta sama, da jiragen yakin Rasha suka kaddamar kan mayakan.

Wani jami’in kungiyar kare hakkin da’adam da ke sa ido a Syria, Rami AbdelRahman ya ce awanni kallilan bayan mayakan suka kame garin, jiragen yakin Rasha suka yi musu barin wutar da ta tilasta musu janyewa.

Ko da yake har yanzu babu cikakkun alkaluman yawan mayakan na IS da sojin Rasha suka hallaka, jami’in kungiyar kare hakkin dan’adam din, Rami, ya ce IS tayi hasarar mayakanta masu yawan gaske.

Sojin Syria da goyon bayan Rasha na cigaba da samun nasarar yakin da suke domin kwato yankunan kasar da suka kufce daga karkashin ikon gwamnatin Bashar al-Assad.

You may also like