
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni sun tabbatar da cewa Kylian Mbappe ba zai buga wa PSG wasan Zakarun Turai da za su buga da Bayern Munich ba.
Hakan ya biyo bayan raunin da ya samu a wasan da suka doke Montpellier 3-1, wanda likitoci suka ce zai shafe makonni uku yana jinya.
Kuma hakan na zuwa yayin da ya rage kasa da mako biyu PSG ta fuskanci Bayern Munich a zagayen kungiyoyin 16.
PSG ce za ta fara karbar bakuncin Bayern Munich a Paris ranar 14 ga watan Fabrairu, kafin su kwashi yan kallo a Alliance Arena da ke Munich ranar 8 ga watan Maris.
Kazalika Mbappe ba zai buga wasan kofin kalubale ba na French Cup da za su buga da Marseille ranar 8 ga watan Fabrairu, da kuma wasan Ligue 1 da Monaco kwanaki uku bayan nan.
Dan wasan gaban ya ci kwallo 25 a wasanni 26 da ya buga wa PSG a bana.