
Asalin hoton, Getty Images
Kylian Mbappe ya ci kwallo biyar a French Cup da Paris St Germain ta caskara Pays de Cassel 7-0 a zagayen ‘yan 16 ranar Litinin.
Pays de Cassel mai buga karamar gasa ta shida a Faransa ta yi nasara cin wasa uku a baya da ya kai ta matakin fafatawa da Paris St Germain.
A minti na 29 ne Mbappe ya fara zura kwallo a raga ya kuma kara hudu daga baya, yayin da Neymar ya ci daya da kuma Soler.
Kawo yanzu Mbappe ya zura kwallo 23 a kakar nan a dukkan fafatawa, ya kuma ci shida daga wasa hudu, tun bayan zura uku rigis a kofin duniya a Qatar.
Mbappe ya ci wa Faransa kwallo uku rigis a gasar kofin duniya a wasan karshe da aka kammala a Disamba, wanda Argentina ta lashe a bugun fenariti.
Wannan shi ne karon farko a tarihi da dan wasa ya ci wa PSG kwallo biyar rigis a tamaula.
Lionel Messi bai buga fafatawar ba, amma Neymar da Mbappe da su aka fara har zuwa tashi daga karawar a kokarin da PSG ke yi na lashe French Cup na 14 jumulla.