MDD ta bukaci a tsagaita wuta a Aleppo


Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a tsagaita wuta na tsawon sa’o’I 48 a garin Aleppo domin bai wa kungiyar agaji isar da kayyakin jinkai ga fararen hula.

Shugaban sashen kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya Jan Egeland, ya ce yanzu haka akwai kungiyoyin agaji da ke cikin shiri domin isar da abinci da kuma sauran kayayyaki ga jama’a.

Majalisar Dinkin Duniya na son tsagaita wutar ne a mako mako domin samun damar shigar da kayan jin kai ga daruruwan fararen hular da ke cikin hali na karancin abinci.

Yankuna 18 ne Majalisar Dinkin Duniya tace dakarun gwamnatin Bashar al Assad suka yi wa Kawanya, kuma uku daga cikinsu ne kawai suka samu tallafi a cikin wannan watan na Yuli.

Majalisar Dinkin Duniya tace Sama da mutane 280,000 aka kashe tun soma yakin Syria a watan Maris din 2011.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like