MDD ta fitar da kudi domin ‘Yan gudun hijirar Boko Haram


 

 

Asusun agajin gaggawa na majalisar Dinkin Duniya ya sanar da sakin kudi da yawansu ya kai dala miliyan 13 domin tallafawa dubun mutanen da ke fama da yunwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ofishin kula da bukatun al’umma na majalisar dinkin duniya karkashin Stephen O-Brien ne ya bayyana sakin kudaden sa’o’i kadan bayan da kungiyar likitoci masu bada agaji ta yi kira ga majalisar Dinkin Duniya bisa bukatar kaddamar da kai agaji ga yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban kwamitin bada agajin gaggawa na hukumar SEMA bangaren Jihar Bauchi, hukumar da ke aiki kafa da kafada da Majalisar Dinkin Duniya, Muhammad Inuwa Bello ya tabbatarwa RFI Hausa da sakin tallafin.

Daruruwan ‘Yan gudun hijirar Boko Haram ne dai ke bukatar tallafi saboda matsanancin hali na karancin abinci.

You may also like