Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a game da sake barkewar kazamin fada a kasar Sudan ta kudu, bayan Gwamnatin kasar ta yi watsi da jita-jitar da ke ta yawo a kasar cewa shugaban kasar Salva Kiir ya mutu.
Majalisar ta ce abin damuwa ne yadda ake ci gaba da samun hargitsi a sassan kasar, da fargaban kar lamarin ya kazance.
Jami’an Majalisar sun kuma koka da yadda ake hana su kai ga wasu wurare da ake rikici a kasar.
Tun ajiya ne dai Ministan Labaran kasar, Michael Makuei, ya fadawa manema labarai cewa shugaba Salva Kiir na nan tangaran, bai mutu ba kamar yadda wasu ke yada wa.