MDD ta Kirayi Kasashe Da Su Zage Damtse Wajen Fada Da Muggan Kwayoyi.


Sakon na Antonio Guterres ya zo ne a ranar fada da fasa kwaurin muggan kwayoyi ta duniya wacce ita ce ranar 26 ga wannan watan na Yuni.

Guterres  Ya kuma kara da cewa; Kokarin da kasashen duniyar za su yi na fada da fasakwaurin muggan kwayoyin zai taimaka matuka wajen samar da ci gaba da kuma zaman lafiya da tsaro a duniya.

Wani sashe na bayanin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya kunshi cewa; Kare hakkin bil’adama yana da bukatuwa matuka da fada da muggan kwayoyi.

Har ila yau, Guterres ya jinjinawa taron da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya yi a shekarar da ta gabata, wanda ya maida hankali akan matsalar muggan kwayoyi a duniya, tare da cewa tsarin da aka bijiro da shi ya yi nazari cikakke akan yadda za a fuskanci matsalar anan gaba.

You may also like