Asalin hoton, Getty Images
Manchester City za ta yi ƙoƙarin kare kofin Champions League a makon nan, inda za ta fara wasan rukuni da kulob ɗin Crvena Zvezda ranar Talata.
Kungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama za ta wakilci Ingila tare da Arsenal da Manchester United da kuma Newcastle, wadda rabonta da gasar ya kai sama da shekara 20.
Kulob ɗin da ya lashe gasar tamaula ta Scotland, Celtic zai buga gasar zakarun Turai karo na biyu a jere.
Batutuwan da suka kamata ku sani kan Champions League 2023/24
Newcastle tana rukuni mai sarƙaƙiya na shida, wanda ya haɗar da Paris St-Germain da AC Milan da kuma Borussia Dortmund.
City na rukuni na uku da ake cewa ba za ta fuskanci ƙalubale ba, da ya ƙunshi RB Leipzig da Red Star Belgrade da kuma Young Boys.
Celtic, wadda ake ganin za ta iya zuwa zagayen gaba, tana rukunin da ya ƙunshi Feyenoord da Atletico Madrid da kuma Lazio.
Manchester United za ta kece-raini a rukunin farko da ya ƙunshi Bayern Munich da FC Copenhagen da kuma Galatasaray.
Arsenal tana rukunin da ya haɗar da ƙungiyar da ta lashe Europa League a kakar da ta wuce, wato Sevilla da kuma PSV Eindhoven da Lens.
Asalin hoton, BBC Sport
Manyan ‘yan wasan da babu su a gasar bana:
Bayan da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka nuna kansu a Turai da taka rawar gani a shekaru da yawa, sai gashi kakar bana ba su a Champions League.
Ronaldo shine na farko da ya koma taka leda a gasar Saudi Arabia – yana kungiyar Al Nassr – shi kuwa Messi yana Amurka a Inter Miami.
Sauran fitattun ‘yan wasan da babu su a Champions League a kakar nan sun hada da dan kwallon Brazil, Neymar da dan kasar Faransa, Karim Benzema, wanda ya koma Al-Ittihad, shi kuwa Neymar na Al Hilal dukkansu a Saudi Arabia.
Ranakun da za a buga wasannin Champions League:
Ranar wasannin farko: 19-20 ga watan Satumba.
Ranar wasa na biyu: 3-4 ga watan Oktoba.
Ranar wasa na uku: 24-25 ga watan Oktoba.
Ranar wasa na hudu: 7-8 ga watan Nuwamba.
Ranar wasa na biyar: 28-29 ga watan Nuwamba.
Ranar wasa na shida: 12-13 ga watan Disamba.
Wasannin zagayen ‘yan 16: 13-14, 20-21 ga Fabraiirun 2024 da kuma 5-6, 12-13 ga watan Maris.
Daf da kusa da na ƙarshe: 9-10, 16-17 April.
Wasan daf da ƙarshe: 30 ga Afirilu, 1 ga watan Mayu, 7-8 ga watan Mayu.
Wasan ƙarshe: 1 ga watan Yuni.
A ina za a buga wasan ƙarshe bana?
Za a buga wasan ƙarshe ne a filin wasa na Wembley da ke Ingila.
Su wa ake sa ran za su iya lashe kofin bana?
An yi hasashen cewar Manchester City ce za ta kara lashe kofin Champions League ba wai Real Madrid ko Bayern Munich ba, in ji wata kididdiga daga Gracenote Euro Club Index, wadda ke auna kokarin kungiyoyi a wasanninsu.
City tana da kaso 37 cikin 100 a damar lashe kofin, Real tana da kaso 13 cikin 100 da kuma Bayern mai kaso 11 cikin 100, haka kuma akwai damar wata sabuwar kungiyar ta lashe kofin da kaso 19 cikin 100.
City da Real da Bayern da kuma Barcelona, dukkansu suna da kaso 90 cikin 100 ta kai wa zagaye na biyu a wasannin bana.
Yaushe za a canja fasalin wasannin Champions League?
Wannan ce kakar karshe daga ita za a sauya fasalin wasannin – Kungiyoyi 32 ne aka raba su rukuni takaws dauke da hur-hudu kowanne, biyu da suka ja ragamar rukuni su kai zagaye na biyu zuwa kwata fainals da daf da karshe da karawar karshe.
Daga kakar 2024-25 kungiyoyi 36 ne za su kece raini a tsakaninsu.