Me ya janyo gagarumar zanga-zangar da ake yi a Isra’ila?



Zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Zanga-zangar ta kasance mafi girma da Isra’ila ta taɓa gani a tarihi

Isra’ila ta shiga wani hali na fuskantar gagarumar zanga-zanga da ba ta taɓa gani ba a tarihi, inda mutane ke adawa da tsarin da gwamnatin ƙasar ke son yi na sauya yadda ɓangaren shari’ar ƙasar ke aiki.

Ga takaitaccen bayani kan abin da ke faruwa a ƙasar a halin yazu.

Me yake faruwa a Isra’la?

Tun farkon wannan shekarar mutane suka fara haɗa manya-manyan zanga-zanga ta mako-mako domin nuna adawa da shirin gwamnati na kawo sauyi a wasu tsare-tsarenta.

Zanga-zangar ta yi ta yaɗuwa, inda dubban ɗaruruwan mutane suka mamaye titunan Tel Aviv – birnin kasuwancin ƙasar – da kuma da wasu birane da garuruwa a faɗin ƙasar.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like