
Asalin hoton, Getty Images
Mamayar da aka yi a 2003 ta janyo kawar da Shugaba Saddam Hussein daga kan mulki
A ranar 20 ga watan Maris ɗin 2003, Amurka da ƙawayenta suka mamayi ƙasar Iraqi tare da hamɓarar da gwamnatin Saddam Hussein.
Amurka ta ce Iraqi na da makaman ƙare dangi kuma hakan barazana ce ga zaman lafiyar ƙasa da ƙasa, amma ƙasashe da dama sun ƙi bayar da haɗin-kai game da iƙirarin Amurka.
Me ya sa Amurka ke son mamayar Iraqi?
A lokacin yaƙin ƙasashen yankin Gulf a 1990-1991, Amurka ta jagoranci rundunonin haɗaka waɗanda suka tirsasa wa sojojin Iraqi ficewa daga ƙasar Kuwait.
Bayan haka, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya yanke shawara, inda yake buƙatar Iraqi ta lalata dukkan makamanta na ƙare dangi.
A 1998, Iraqi ta dakatar da wata haɗaka da ta ke yi da masu sa ido na mallakar makamai na MDD, inda Amurka da Birtaniya suka mayar da martani kan haka da harba makamai ta sama.
Bayan harin ƙungiyar al-Qaeda kan Cibiyar Kauwanci ta Duniya da ke birnin New York da kuma shelkwatar tsaro ta Pentagon a birnin Washingtn DC a ranar 11 ga watan Satumban 2001, gwamnatin shugaba George Bush ta soma shirin mamayar Iraqi.
Shugaba Bush ya yi iƙirarin cewa Saddam Husseini na ci gaba da sarrafawa da kuma mallakar makaman ƙare dangi, kuma Iraqi na cikin ƙasashen da ta ayyana masu mummunar aƙida tare haɗe da Iran da kuma Koriya Ta Arewa.
A watan Oktoban 2002, Majalisar Dokokin Amurka ta amince da amfani da ƙarfin soji kan Iraqi.
“Yawancin mutane a Washington na da yaƙinin cewa akwai ƙwararan hujjoji da suka nuna cewa Iraqi ta mallaki makaman ƙare dangi, kuma hakan barazana ce,’’ in ji Dakta Leslie Vinjamuri, daraktar wani shirin Amurka a Chatham House da ke Landan.
A watan Febrairun 2003, sakataren harkokin wajen Amurka na wancan lokaci Colin Powell ya buƙaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya bayar da damar amfani da sojoji kan Iraqi, inda ya ce ƙasar na saɓawa shawarwarin da aka cimma da ita kan makamanta na ƙare dangi.
Sai dai, bai gamsar da Kwamitin ba. Yawancin mambobin kwamitin na son masu sa ido kan makamai na MDD da kuma na Makamashi – da suka je Iraqi a 2002 – su gudanar da ƙarin bincike a can domin samun hujjoji.
Amurka ta ce ba za ta jira rahoton masu sa idon ba, inda ta haɗa rundunar haɗaka don mamayar Iraqi.
Su waye suka mara wa yaƙin baya?
Cikin ƙasashe 30 da suka shiga haɗakar, har da Birtaniya da Australiya da Poland cikin waɗanda suka yi mamayar.
Birtaniya ta aike da dakaru 45, 000, inda Australiya ta aike da 2,000 sai kuma Poland da ta tura dakaru na musamman guda 194.
Kuwait ta bari an fara mamayar daga yankinta.
Sifaniya da Italiya sun bayar da taimakon diflomasiyya ga dakarun haɗaka da Amurka ta jagoranta tare da ƙasashen gabashin Turai da dama, waɗanda suka ce suna da yaƙinin cewa Iraqi na da makaman ƙare dangi da suka saɓa shawarwarin da aka cimma a taron MDD.
Waɗanne irin zarge-zarge Amurka da Birtaniya suka yi wa Iraqi?
Sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya faɗa wa Majalisar Dinkin Duniya a 2003 cewa Iraqi na da ɗakunan gwaje-gwaje da ta ƙirkiro na ƙera makamai.
Sai dai, a 2004 ya bayyana cewa waɗannan ba ƙwararan hujjoji bane da za a iya yarda da su.
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka Colin Powell ya faɗa wa MDD cewa Iraqi na ƙera makaman ƙare dangi
Gwamnatin Birtaniya ta fito da wani rahoto, inda ta ke iƙirarin cewa Iraqi ta shirya makaman roka da za ta yi amfani da su wajen kai mata hari cikin mintuna 45 a yankin gabashin tekun Mediterranean.
Firaministan Birtaniya a lokacin Tony Blair, ya ce babu tantama kan batun cewa Saddam Hussein na ci gaba da ƙera makaman ƙare dangi.
Ƙasashen biyu sun dogara ne kan iƙirarin wasu mutanen Iraqi biyu da suka yi tawaye – wani injiniya mai suna Rafid Ahmed Alwan al-Janabi da kuma wani jami’in leƙen asiri mai suna Maj Muhammad Harith – waɗanda suka ce suna da dukkan bayanai kan makaman ƙare dangi na Iraqi.
Sai dai, daga baya mutanen biyu sun ce ƙirƙiro da hujjojin suka yi saboda suna son ƙawayen su mamayi Iraqi da kuma kawar da Saddam.
Wa ya ƙi mara wa yaƙin baya?
Wasu makwaɓtan Amurka guda biyu, Canada da Mexico sun ki mara wa yaƙin baya.
Jamus da Faransa da suka kasance manyan ƙawaye a Turai, su ma sun ki bayar da goyon baya ga yakin.
Ministan harkokin wajen Faransa Dominique Villepin, ya ce bayar da taimakon soji zai zamo abin da bai kamata ba.
Ita ma Turkiyya – ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar Nato da kuma ke makwaɓtaka da Iraqi – ta ƙi barin Amurka da ƙawayenta su yi amfani da sansanonin sojojinta.
Ƙasashen yankin Gabas Ta Tsakiya da suka mara wa Amurka da Iraqi baya a 1990-91 a lokacin yaƙin Gulf, kamar Saudiyya, sun ƙi amincewa da mamayar Iraqi a 2003.
“Da farko ƙasashen yankin Gulf sun ɗauki mamayar da wasa,’’ in ji Farfesa Gilbert Achcar, wani masanin siyasar Gabas Ta Tsakiya a jami’ar Landan SOAS.
“Sun damu da cewa Iran na samun iko kan Iraqi bayan kawar da gwamnatin Saddam Husseini.”
Me ya faru a lokacin yaƙin?
A safiyar ranar 20 ga watan Maris ɗin 2003, sojojin Amurka 295, 000 tare da sojojin ƙawance suka ƙaddamar da mamaya kan Iraqi ta iyakar ƙasar Kuwait.
Mambobi 70,000 da mayaƙan Ƙurdawa sun fafata da sojojin Iraqi a yankin arewacin ƙasar.
A watan Mayu, aka ci galabar sojojin Iraqi tare da hamɓarar da gwamnatin ƙasar…daga baya kuma aka cafke Saddam Husseini da gabatar da shi gaban kotu da kuma zartad da hukuncin kisa a kansa.
Sai dai babu wani makami na ƙare dangi da aka samu a Iraqi.
A 2004, ƙasar ta faɗa cikin rikicin ƴan ta-da-ƙayar-baya. Shekaru bayan haka, yaƙin basasa ya ɓarke a ƙasar tsakanin ƴan ƙabilar Sunni da kuma ƴan Shi’a.
Sojojin Amurka sun janye daga Iraqi a 2011.
An ƙiyasta cewa mutum 461, 000 ne suka mutu a Iraqi sanadiyyar yaƙe-yaƙe tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2001, inda kuma aka ce yaƙin ya janyo asarar dala tiriliyan uku.
“Amurka ta rasa ƙimarta daga wannan yaƙi,” in ji Dakta Karin von Hippel, babban-darakta a wata cibiya mai suna think tank da ke Landan.
“Za ka ji mutane na cewa shekaru 20 bayan mamayar: me ya sa za mu amince da bayanan sirrin Amurka?”