Me ya sa Isra’ila ta raba Gaza zuwa ɓangare biyu?v

Asalin hoton, GETTY IMAGES

A ranar Lahadi, mai magana da yawun sojojin Isra’ila, Daniel Hagari ya ce “Yanzu akwai Gaza ta arewa da Gaza ta kudu.”

Bayanin Hagari ya zo ne a daidai daren da Isra’ila ta yi gagarumin ruwan wuta a Gaza wanda ya yi sanadin katsewar Intanet, kamar yadda wakilin BBC a Gaza, Rushdi Abualouf ya ruwaito.

Shugaban asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza ya ce mutane sun riƙa ɗauko gawawwaki a kan jakuna da motocinsu kasancewar motocin asibiti ba sa aiki.

Rundunar sojin Isra’ila ta nace kan cewa Hamas na amfani da asibitoci a arewacin Gaza domin ayyukansu, sai dai shugaban asibitin na Al-Shifa ya musanta hakan, inda ya ce a shirye suke su bari Majalisar Dinkin Duniya ta duba asibitin.

Ya zuwa farkon wannan mako, yawan mutanen da aka kashe a Gaza tun bayan da Isra’ila ta fara ruwan wuta ya zarce 10,022, kamar yadda ma’aikata lafiya ta yankin ta bayyana.

Isra’ila ta mamaye hanyoyi

gf

Asalin hoton, EPA

An ga tankokin yaƙin Isra’ila a kan babbar hanyar da ake kira Saladin a Zirin Gaza, wadda ta haɗa arewaci da kudancin yankin.

Wakilin BBC, Paul Adams ya ce da alama ɗaya daga cikin manyan manufofin Isra’ila shi ne raba Gaza zuwa yanki biyu, wato arewaci da kudanci.

Rahotanni sun bayyana cewa an riƙa gwabza faɗa a wasu ɓangarori na babbar hanyar Saladin.

An kai hari kan wasu gine-gine a yankin, kamar asibitin ‘Turkish Friendship Hospital.

An kuma lalata wasu gine-ginen gaba ɗaya, ciki har da jami’ar Al-Azhar da wasu gine-gine na alfarma waɗanda ƙasashen Moroko da Saudiyya suka ɗauki nauyin samarwa.

Haka nan ma a ƙarshen makon jiya an ga motocin sulke na Isra’ila a ɗaya hanyar da ta haɗa yankunan biyu, wadda ake kira Al Rashid, kamar yadda Adam ya bayyana.

Wasu labaran da za ku so ku karanta:

Hare-hare a faɗin Gaza

dfc

Asalin hoton, REUTERS

Bayanan hoto,

Sakataren harkokin waje na Amurka, Antony Blinken

Duk da kiraye-kirayen Isra’ila na cewa mutane su yi ƙaura daga arewacin Gaza zuwa kudanci, Isra’ilar ta ci gaba da kai hare-hare a duka ɓangarorin biyu.

A ranar Asabar Isra’ila ta kai hari a sansanin ƴan gudun hijira na Maghazi, wanda ke a tsakiyar Gaza.

Yanzu haka firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa za a ci gaba da ƙaddamar da hare-hare a Birnin Gaza wanda aka yi wa ƙawanya.

Isra’ila ta ci gaba da ƙarfafa wa mutanen arewacin Gaza su 300,000 gwiwa kan cewa su koma kudu, sai dai waɗanda ba su son yin hakan ko kuma wani abu ya sanya suka gaza barin yankin sun tsinci kansu a tsakiyar ƙazamin yaƙi.

Mummunan halin da waɗanada aka yi garkuwa da ƴan’uwansu ke ciki

An buɗe mashigar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar domin bai wa ƴan ƙasashen ƙetare da kuma waɗanda suka samu munanan raunuka damar tsallakawa.

Rafah ta kasance hanya ɗaya tilo da al’ummar Gaza za su iya fita daga yankin tun bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma hare-haren ramako da Isra’ila ta ƙaddamar.

A ɗaya ɓangaren kuma a Isra’ila ana ci gaba da matsa wa gwamnati lamba kan ta lalubo hanyar sako mutanen da ake garkuwa 240 – waɗanda cikin su akwai mata da yara da tsofaffi – waɗanda Hamas ta kame a lokacin harin da ta kai, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 1,400.

Adva Adar, wanda kakarsa mai shekara 85 a duniya ke cikin waɗanda Hamas ke garkuwa da su, ya shaida wa BBC cewa yana da yaƙinin cewa manufar hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ita ce domin ceto mutanen da ake riƙe da su a Gaza.

Ya ce “Idan Isra’ila za ta ƙaddamar da hari ta ƙasa a Gaza, to za su yi hakan ne domin ceto waɗanda ake garkuwa da su.”

Saƙon Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya koma ƙasashen Gabas ta tsakiya.

A ranar Litinin ya je birnin Ankara, babban birnin Turkiyya, inda ya gana da shugabannin Turkiyya.

Ya tabbatar wa shugaban Falaɗinawa, Mahmoud Abbas cewa gwamnatinsa za ta karɓe iko da Gaza bayan yaƙin.

Ya kuma yi tir da tashin hankalin da ake samu a Gaɓar Yamma, inda ya ce suna son a rage yawan fararen hula da ke mutuwa a Gaza da kuma bunƙasa yanayin rayuwa.

Ya kuma jaddada goyon bayan Amurka ga Isra’ila ɗari-bisa-ɗari ta fannin soji da diflomasiyya amma ya ce dole ne a martaba dokar ƙasa da ƙasa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like