Me ya sa yunkurin yujin mulkin Turkiyya ya ci tura?


Kawo yanzu an kama mutane kusan 6,000 kama daga dakarun soji zuwa jami’an shari’a da sauran jami’an gwamnati a Turkiyya, bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da ya ci tura ranar Juma’a.

Ba wannan ne karo na farko da sojojin Turkiyya suka yi kokarin wargaza dimokradiyyar kasar ba.

Sun kwace ikon kasar sau da yawa a cikin shekaru 50 da suka gabata.

A wannan karon akwai abubuwa da dama da suka jawo rashin nasarar juyin mulkin da sojojin suka yi yunkurin yi a ranar Juma’a.

Ziya Meral, wani mai sharhi a Cibiyar nazari kan tarihi da bincike kan rikice-rikice.

Ya kuma bayyana dalilai biyar da suka sa juyin mulkin bai yi nasara ba.

1. Rashin samun goyon bayan mutanen gari

Duk da cewa masu yunkurin juyin mulkin sun fara kamfe dinsu wajen ganin sun hada kan jama’a don nuna adawa da gwamnati, hakan bai yi wani tasiri ba.

Mafi yawan al’ummar kasar sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan yunkuri, sun kuma ki bayar da cikakken hadin kai.

Haka ma jam’iyyun adawa da dama kamar CHP da MHP sun ki bayar da hadin kai, saboda basa so a maimaita wahalar da kasar ta shiga a can baya sakamakon juyin mulki.

2. Rashin isassun sojoji

Idan har ana son samun nasarar juyin mulki, to dole ana bukatar goyon bayan dakarun tsaro. Sai an samu goyon baya daga mafi yawan sojojin kasar a dukkan biranen Turkiyya.

Duk da cewa tankokin yaki sun mamaye tituna a birnin Santanbul, al’amarin bai kai gaci ba saboda hafsan sojin kasar Janar Hulusi Akar, bai bayar da goyon baya ba, al’amarin da yasa masu shirya juyin mulkin suka tsare shi.

Shi ma kuma shugaban sojoji a birnin Santanbul bai bayar da hadin kai ba.

3. Wasu hukumomin gwamnati basu goyi baya ba

Kazalika, rashin samun goyon bayan manyan hukumomin gwamnati masu karfi da kuma wasu manyan jami’am gwamnatin, ya jawo cikas wajen cikar burin sojojin da suka kuduri niyyar wannan juyin mulki.

Al’amarin da yasa yunkurin na su bai yi tasiri ba.

4. Kasashen duniya sun yi Allah-wadai

Rashin samun hadin kan manyan kasashen duniya masu karfin fada aji ya taimaka wajen rashin nasarar juyin mulkin.

Haka kuma kasahse irinsu Amurka sun yi Allah-wadai da yunkurin juyin mulkin.

Shugaba Obama ya kuma yi kira ga dukkan bangarori da su goyi bayan gwamnatin dimokradiyya ta Turkiyya.

Haka kuma Amurkar ta tabbatar wa Turkiyya cewa tana goyon bayanta wajen ganin tabbatar dimokradiyyarta.

5. Rashin cikakkiyar manufa

Sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin ba su da cikakkiyar manufa, saboda sun ce suna so su tabbatar da tsarin dimokradiyya ne, amma kuma sai ga shi tashin farko sun kai wa majalisar dokokin kasar hari.

A tsari na gaskiya, duk mai son tabbatar da tsarin dimokradiyya, to ba zai kai wa majalisar dokoki hari ba, tun da ita ce ginshikin dimokradiyyar kowacce kasa.

Ko ina duriyar Erdogan a lokacin yunkurin juyin mulki?

Bayan sa’o’i da dama a loakcin da aka yi yunkurin juyin mulki ba a ji duriyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan ba.

Rahottani sun ce yana hutuwa a wajen shakatawa na Aegean da ke Kudu Maso Yammacin kasar.

Sai dai kanwa-ta-kar-tsami a lokacin da shugaban ya dira a filin jirgin Ataturk da ke birnin Santanbul ya kuma yi jawabi ga manema labarai.

Jim kadan da saukarsa sai ta bayyana cewa, gwamnati na rike da ikon kasar da kuma goyon bayan manyan jami’an soji.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like